Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hawan Ɗorayi


Gabatarwa

Wannan hawa shi ne cikamakon hawan bukukuwan Sallar Azumi a Kano. Ana yin sa a rana ta biyar da salla. Kenan, ranar ɗaya da biyu ana Hawan Idi da na Daushe. Rana ta uku hutu, rana ta huɗu kuma Nassarawa, sai kuma ta biyar a je Ɗorayi. Hawa ya ƙare kenan sai kuma a jira sallar layya.

Idan sarki ya yi hawa daga cikin gida a wannan rana ta Hawan Ɗorayi, yakan fito ne ta Ƙofar Ƙwaru. Daga nan sai ya saka gabansa Yamma ya hau Titin zuwa Mandwari, sai Tal’udu, sai Kwanar FCE. Sai ya karyaka Kudu ya fita ta Ƙofar Fanfo ya tsallaka titi ya shiga ya yi ta tafiya har sai ya je Ƙarshen Waya; ƙarshen kantagar tsohuwar jami’ar Bayero daga Kudu a shashen Gabas. Sannan ya raɓa ta jikin katangar Kudu ta jami’ar har sai ya je mararrabar gidan mahaukata na Ɗorayi sannan ya karyaka ya ƙarasa ƙofar gidan sarki na Ɗorayi ya ja ya tsaya. Idan ya tsaya sai hakiman sarki su riƙa zuwa da sukuwa suna jeruwa a gefen hagu da dama har sai sun gama zuwa. Sai sarki ya sauka ya bi ta tsakiyar su ya shiga gida. Sannan suma kowa ya sauka.

Bayan sarki ya ɗan huta, sai kuma ya fito fadarsa ta gidan ya zauna. Hakimai da sauran masu riƙe da muƙaman sarauta duk suma sai su fito su zo su yi gaisuwar kamar yadda aka saba a fada sannan su zauna.

Bayan fada ta tashi, sai kowa ya koma masauki. Idan aka yi sallar La’asar, sai kuma a sake hawa a koma gida. Da farko za bi ta hanyar da aka tafi har zuwa shatale-talen Ta’uludu. Idan aka zo nan, sai sarki ya karya zuwa Hagu (Arewa) ya bi titin Malam Aminu Kano har zuwa mararrabar gidan-yari da ke Gwauron Dutse, sannan ya karyaka Dama ya shiga titin gidan Nababa ɗoɗar har zuwa mararrarbar Kasuwar Kurmisannan ya karyaka zuwa Bakin Zuwo, zuwa Tudun Nufawa har zuwa mararrabar titin Soron Ɗinki sannan ya juya Kudu ya nufi gidan Shatima. Idan ya zo gidan Shatima sai ya ja ya tsaya. Hakimai su gama wuce shi suna sukuwa su je su jira shi kaɗan a Ƙofar Ƙwaru. Idan suka gama jeruwa kamar yadda suka yi a Ɗorayi hagu da dama, sai sarki ya zo ya sauka ya ratsa ta tsakiyar su ya shiga gida.

Manazarta:


Gwangwazo (2004). Gamzaki mai Asubahi, In Ya fito Gari Ya Waye, Sarkin Kano Alhaji (Dr.) Ado Bayero.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub